Gwamnatin tarayya ta kwace lasisin hako ma’adanai guda 1,633 aka baiwa kamfanonin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatin tarayya ta kwace Lasisin hako Ma’adanai guda 1,633 da aka baiwa kamfanonin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Ministan ma’aikatar ma’adanai, Dele Alake ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja

A cewarsa, jami’an tsaro tare da hadin guiwar hukumar kula da ma’adinai ta ma’aikatar, an basu izinin kamo duk wanda aka samu da laifin karya dokar.

Alake ya bayyana cewa, an soke lasisin hakar ma’adinan ne saboda rashin biyan harajin shekara da aka kayyade akan lokaci.

Ya kara da cewar, duk da lamunin kwanaki 30 da ofishin ma’adinai na Cadastral ya bayar, amma kamfanonin sunki biyan hakkin gwamnati daya rataya akansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *