Buhari ya bayyana cewar ba don rufe iyakar Najeriya da Nijar da akayi ba, da tuni ya bar Najeriya

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ba don rufe iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar da akayi ba, da tuni ya bar Najeriya

A hirarsa ta farko tun bayan saukarsa daga mulki, Burahi ya shaidawa  gidan talabijin na kasa (NTA), cewa duk da cewa bashi bane sugaban kasa, har yanzu mutane basu barshi ya huta ba, inda kullum suke zuwa suna takura masa.

Buhari wanda ya mika mulki ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu Mulki a ranar 29 ga watan Mayu, yace yayi iya kokarinsa a cikin a mulkin da yayi.

Ya kara da cewa ’yan kasarnan suna da wuyar sha’ani wanda hakan yasa shugabantar suke da wahalar gaske, amma duk da haka, yayi iya kokarinsa.

Yace ya kamata masu sukar gwamnatinsa su yiwa kansu tambaya kan rawar da kowannensu ya taka a wajen yakar cin hanci da rashawa.

Buhari ya bayyana cewa ya nada mutane kuma ya basu damar gudanar da ayyukansu a lokacin daya basu ayyuka, yana mai jaddada cewa idan da za’a a sake bashi dama, ba zai yi wani abu daban ba’a tsarin Najeriya a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *