Kadarori da abubuwa masu amfani sun kone a wani sashi na gidan marigayi Alhaji Shehu Shagari, tsohon shugaban kasar Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne misalin karfe 11 na safiyar jiya Lahadi a gidansa da ke Gobirawa a Sokoto.
Akalla mutane 20 yan uwan marigayin tsohon shugaban kasan ne a cikin gidan lokacin da lamarin ya faru.
A cewar wadanda abin ya faru a kan idonsu, kadarori da dama mallakar iyalan maraigayin shugaban kasar sun kone a gobarar, amma ba a rasa rayuka ba.
Shagari ne mutum na farko da aka fara zaba a matsayin shugaban kasa karkashin dimokradiyya. Ya rike mukamin daga 1979 zuwa 1983 lokacin da aka masA juyin mulki. Ya kuma rasu yana da shekaru 92 a ranar 28 ga watan Disamban 2018.