Hukuncin Zaben Kano: Rundunar ’yan sandan Kano ta gargadi masu neman shirya zanga-zanga ko tatttakin a jihar kan hukuncin kotun.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ba za ta raga wa masu neman tayar da tarzoma a jihar nan kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamnan jihar ba.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hussaini Muhammad Gumel, ya gargadi masu neman shirya zanga-zanga ko tatttakin a jihar kan hukuncin kotun da cewa duk wanda runduna ta samu yana karya doka a jihar, zai yaba wa aya zaki.

Kakakin rundunar, SP Abdulahi Haruna Kiyawa, ya ce gargadin yana da muhimmanci saboda rahotannin da suka samu kan yadda magoya bayan wata jami’iyya ke amfani da wasu hanyoyiyn bayan fage wajen kiran jama’a da su fito kan titunan Kano domin zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka karar.

A ranar Juma’a 17 ga wata ne Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta kara kwace kujerar Gwamnan  Kano daga hannun Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP, bisa hujjar rashin kasancewarsa dan jam’iyyar kafin zaben da ya kai shi kan kujerar.

Don haka kwamishinan ya shawarci Kanawa da su kwantar da hankalinsu, amma su guji duk wani haramtaccen tattaki ko zanga-zanga ko tashin hankali da aka kira su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *