’Yan Boko Haram Sun Kashe Dan Sanda A Tawagar Gwamnan Yobe

Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari kan ayarin motocin Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, inda suka kashe dan sanda daya.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a kan ayarin a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Asabar, sannan aka jikkata wasu ’yan sandan su biyu.
Gwamnan na kan hanyarsa ce ta komawa Damaturu bayan ya halarci taron yaye dalibai karo na 24 na Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno.
A cewar wani ganau da ke cikin tawagar da ya nemi a sakaya sunansa, maharan sun bude wuta kan ayarin motocin daga bangarorin biyu na babbar hanyar, inda suka nufi direbobin motar.
Majiyar ta ce “Mun tsira da kyar a yau, an kai wa ayarin motocinmu hari ne a tsakanin garin Beneshiekh da Mainok mai tazarar kasa da kilomita 60 zuwa Damaturu bayan halartar taro karo na 24 na yaye daliban Jami’ar Maiduguri.
Sai dai Gwamna Buni ba ya cikin ayarin motocin a lokacin da lamarin ya faru kasancewar ya tafi Abuja ne domin gudanar da wani aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *