Gwamnonin yankin arewa maso yammacin Najeriya sun gana da shugaban Bankin Raya Afirka inda suka nemi tallafin bankin wajen haɓaka harkokin noma.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar Zamfara ta ce gwamnan jihar, Dauda Lawal. ya nemi bankin ya kafa wata da’irar harkokin noma da masana’antu da zimmar sarrafa amfanin da aka noma a cikin gida.
“Yayin tattaunawar da gwamnonin Zamfara, da Kebbi, da katsina, da Jigawa, da Kano, da Kaduna suka yi da shugaban bankin Akinwumi Adesina, sun faɗa masa yankunan da suka fi buƙatar tallafi.
Gwamnonin sun nemi agajin bankin ne don ya tallafa musu wajen daƙile ƙalubalen da suka haɗa da tsaro, da inganta rayuwa, da kuma noma, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ta ƙara da cewa bankin ya nuna sha’awarsa ta tallafa wa jihohin, inda “shugaban bankin ya jinjina wa gwamnonin game da fifita walwalar al’ummarsu.