Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki alkawarin cewa gwamnatinsa za ta karawa Sarakunan gargajiya karfi a dokar kasa.
Shugaba Tinubu ya ce zai yi aiki da ‘yan majalisar tarayya domin a ba Sarakuna aiki a tsarin mulki.
Shugaban kasar ya dauki wannan alwashi ne wajen taya Mai martaba Oba Victor Kiladejo murnar cika shekara 70 a duniya.
Tinubu wanda ya samu wakilcin Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo zuwa wannan biki da aka shirya, ya jaddadawa Sarakunan gargajiya cewa gwamnati mai-ci za ta yi aiki da su. .
Rahoton ya ce gwamnatin Tinubu ta na ganin Sarakunan gargajiya suna da rawar takawa wajen kawo tsaro da zaman lafiya a kasarsu.
Haka zalika nauyin kare al’adar gargajiya ta rataya ne a kan wadannan Sarakuna.