Shugaba Bola Tinubu ya ce ya kuduri aniyar sauya tarihin Najeriya domin amfanin ‘yan Najeriya baki daya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala aikin ibadar Umrah a ranar Lahadi a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar sauya labarin ta hanyar yin gyare-gyare da tsare-tsare da manufofin da a karshe za su amfani ‘yan kasa baki daya.