INEC ta bayyana Ahmed Usman-Ododo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana Ahmed Usman-Ododo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi.

Ododo ya samu ƙuri’a 446,237, inda ya doke mai biye masa, Muritala Ajaka na jam’iyyar SDP, wanda ya samu ƙuri’u 259,052.

Dino Melaye na PDP ne ya zo na uku, inda ya samu ƙuri’u 46,362.

Hakan na nuna cewa Ahmed Ododo ya doke dukkanin ƴan takara 18 da suka fafata a zaɓen gwamnan jihar ta Kogi wanda aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Shi dai Usman-Ododo ba kowa ne ya san shi ba gabanin nasarar da ya samu a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC.

A lokacin zaɓen fitar da gwani, Ododo ya doke ƴan takara kama Shu’abu Audu, Stephen Ochen, Sanusi Ohiare da kuma Smart Adeyemi.

Jihar Kogi na daga cikin jihohi uku da aka gudanar da zaɓe a cikinsu ranar Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *