Hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya, Inec, ta ce tana bincike kan ƙorafin da ake kan wasu takardun rubuta sakamakon zaɓe da aka cike tun kafin fara kaɗa ƙuri’a a jihar Kogi.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Ƙungiyar sa-ido kan zaɓuka da kyautata dimokuraɗiyya ta Yiaga Africa ta ce lamarin ya faru ne a rumfar zaɓe mai lamba PU 004, Eni Ward da ke ƙaramar hukumar Ogori/Magongo.
Ƙungiyar ta wallafa wani hoto da ake zargin na sakamakon zaɓen rumfar ne da aka riga aka cike, tana mai kira ga hukumar zaɓe ta Inec da ta bincika lamarin.
Shi ma ɗan takarar gwamnan Kogi na PDP, Sanata Dino Melaye, ya yi irin wannan zargi cikin wani bidiyo da ya wallafa.