Gwamnati zata gina gidaje 10,000 a kashi na farko na shirin Tinubu kan samar da gidaje ga alumma a Abuja

Gwamnatin tarayya ta ce za a gina gidaje kusan 10,000 a kashi na farko na shirin Shugaban Kasa Tinubu kan samar da gidaje ga alumma a babban birnin tarayya.

Ministan gidaje da raya birane, Arc. Ahmed Dangiwa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake duba gidajen da ma’aikatar ta gina da hukumomin da ke karkashin ma’aikatar a Abuja.

Dangiwa a daya daga cikin wuraren da ya duba gidaje kusan 1,250 da bankin bayar da lamuni na gwamnatin tarayya a Dei-dei, ya ce za a gina sama da gidaje 40,000 a kashi na farko na shirin a fadin kasa baki daya kana ya ce Za a samar da rukunin gidaje masu araha ga masu karamin karfi da matsakaita da kuma masu hannu da shuni a birnin tarayya Abuja.

Ministan gidaje da raya birane, Arc. Ahmed Dangiwa, Ya gargadi ’yan kwangilar da suka yi watsi da ayyukansu da su koma bakin aiki ko kuma su rasa aiyukan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *