Gobara ta lalata kayyakin miliyoyin naira a wata kasuwar dake jihar Osun

Wata mummunar gobara da ta tashi a safiyar ranar Asabar ta lalata kayyakin miliyoyin naira a Oja Tuntun da ke Ile-Ife a jihar Osun.

Har yanzu dai ba a san musabbabin aukuwar lamarin na baya-bayan nan a kasuwar ba. Sai dai mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Osun, Adekunle Ibrahim ya ce sun samu kiran waya da misalin karfe 12:30 na safe daga wani mazaunin kusa da kasuwar.

Ibrahim ya kara da cewa a lokacin da ‘yan kwana-kwana suka isa wurin, gobarar ta shafi wani gini da ke dauke da shaguna 16 da kwantena a cikin kasuwar, inda ya kara da cewa tawagar hukumar kashe gobara ta jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife ita ma ta shiga cikin aikin.

Ya ce, “An sanar da ofishin kashe gobara na shiyyar Ile-Ife game da wata gobara da ta tashi a sabuwar kasuwar Olulere, Oja Tuntun a Ile-Ife da misalin karfe 12:30 na safiyar ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.

“Mutanenmu sun isa wurin da gobarar ta mamaye kasuwar sosai kuma suka kashe gobarar tare da taimakon sashen kashe gobara na jami’ar OAU.

“Gobarar ta lakume kaddarorin da suka kai sama da Naira miliyan 500, amma wani shingen da ke da jimillar shaguna 16 da kwantena daya, wanda hakan ya sa aka samu shaguna 17.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *