Dino Melaye ya bukaci INEC ta soke zaben kananan hukumomi 5

Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kogi, ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta soke zaben kananan hukumomi biyar na jihar saboda abinda ya kira runton kuri’u da kuma sayen masu zabe da kudi.

Melaye ya bayyana kananan hukumomin da abin ya shafa da su ne Okene, Okehi, Ajaokuta, Adavi, da Ogori/Mangogo, yana mai cewa an tabka magudi a sakamakon zaben.

Dole ne INEC ta soke zaben a kananan hukumomi 5 na Kogi-Tsakiya. Zaben da aka yi a Okene, Okehi, Ajaokuta, Adavi, da Ogori/Mangogo wata zamba ce da aka hada kai daga babban mataki na INEC Melaye ya wallafa a shafinsa na X.

Tun da farko, wata kungiyar farar hula mai suna YIAGA Africa, ta yi tsokaci kan gano sakamakon zabe daga sashin zabe na 004 da ke Eni Ward na yankin Ogori/Mangogo.

An ga sakamakon jabun yayin da masu kada kuri’a ke cikin jerin gwano,sai kuma ga sakamakon mazabar a hannun wasu suna yayatawa a kafafen sadarwa.

A sakamakon zaben, wanda aka makala kwafinsa a kan yanar gizo ya nuna cewar Jam’iyar APC ta samu kuri’u 200; AA ta ci 1; yayin da ADC, PDP da SDP suka samu kuri’u 2 kowanne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *