Kotu ta bayar da umarnin cewa a saki tsohon gwamnan CBN, Emefiele.

Wata kotu a kasarnan ta bayar da umarnin cewa a saki tsohon gwamnan babban bankin Njaeriya Godwin Emefiele ba tare da an gindaya wani sharadi ba, ko kuma akai shi kotu a ranar Laraba domin sauraron bukatarsa ta neman beli.

Tsohon gwamnan CBN din bai bayyana a gaban kotu baa jiya Litinin lokacin zaman sauraron bukatarsa ta neman beli wanda hakan ya sanya alkalin kotun Olukayode Adeniyi, ya bukaci hukumar EFCC da lauyoyin gwamnati da cewa su sake shi ko kuma su kawo shi kotu cikin kwana biyu.

An tsare Emefele mai shekaru 61 da haihuwa a ranar 10 ga wayan Yuni, bayan zarginsa da almundahana wajen siyo wadansu kayayyaki.

Tunda farko hkukmar DSS ne suka tsare shi bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba ind daga baya suka yi watsi da wannan zargin.

A ranar Litinin hukumar EFCC ta bayyana cewa ya kwashe mako guda a hannunta.

Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya sauke shi daga mukaminsa a ranar 9 ga watan Yuni inda daga baya hukumar DSS ta kama shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *