INEC, ta bayyana shirinta na gudanar da zaben gwamnonin jihohin Bayelsa, Kogi da Imo a watan nuwamba

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana shirinta na gudanar da zaben gwamnonin jihohin Bayelsa, Kogi, da kuma Imo a ranar 11 ga watan nuwamba.

Darakta mai kula da wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri’a ta INEC, Mary Nkem, ta bayar da wannan tabbacin ne a wani dakin taro na jama’a kan harkokin zabe a Abuja.

Nkem ta ce an kula da duk wasu kura-kurai da aka samu a babban zaben da aka yi a farkon shekarar.

Ta ce INEC ta tanadi tsare-tsare da dama don tabbatar da fara tura wasu muhimman kayyayaki zuwa rumfunan zabe, ciki ha da jami’an wucin gadi da suka yi zango a kusa da rumfunan zabe kwana guda kafin gudanar da zaben.

INEC

Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargaɗi ma’aikatansa da suyi aiki da gaskiya wurin gudanar da zaɓen gwamnoni da za’ayi a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa a ranar Asabar mai zuwa.

Yakubu ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin daya  kai wata ziyara don tabbatar da irin shirin da akayi wajen gudanar da zaɓuɓɓukan a jihohin.

Shugaban ya tabbatar da cewa, zaa biya dukkanin ma’aikatan dukkan alawus ɗinsu kafin a fara zaɓen.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa wacce ke ɗauke da rahotannin aikace-aikacen INEC na yau da kullum, wadda hukumar ke wallafawa.

Yakubu ya ƙara da cewa, INEC ta himmatu sosai wajen wanzar da ingantacce kuma sahihin zaɓe a jihohin uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *