Gwamnatin tarayya ta kwaso ‘yan Najeriya 161 da suka makale a Libya

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya IOM sun kwaso ‘yan Najeriya 161 da suka makale a kasar Libya a ranar Talata.

Ambasada Kabiru Musa, mai kula da ofishin jakadancin Najeriya a kasar Libya, ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce makasudin gudanar da atisayen ‘yan gudun hijira na son rai, shi ne tabbatar da cewa ‘yan Najeriya da ke gudun hijira ba su makale a kasashen waje.

“Wadanda aka kwaso sun taso ne daga filin jirgin saman Mitiga na kasa da kasa da ke birnin Tripoli a cikin wani jirgin da aka yi hayarsa a ranar Talata kuma ana sa ran za su isa filin jirgin na Murtala Mohammed da ke Legas da rana.

“Wadanda aka kwaso sun kasance mata manya 100, manya maza 37, yara 16, da jarirai takwas.

“Jami’ai za su karbe su idan sun isa wurin domin saukaka musu matsuguninsu da kuma komawa cikin al’umma,” in ji Musa.

Ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa babu wani dan Najeriya da zata bari ya makale ko kuma a bar shi a wuraren da ake tsare da su a Libya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *