“Gargadin da ofishin jakadancin kasar Amurka yayi abune mai tayar da hankali daka iya shafar tattalin arzikin Najeriya” – FG

Gwamnatin tarayya tace gargadin da ofishin jakadancin kasar Amurka yayi a karshen makon daya  gabata cewar yan kasarsa su lura da otal-otal din da zasu zauna domin samun yiwuwar kai hare-hare, abune mai tayar da hankali daka iya shafar tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnatin tarayya, ta bayyana hakan ne ta bakin ministan yada labarai, Alhaji Muhammad Idris, wanda yace babu abinda hakan zai haifar sai tsananin fargaba ga kowa.

Yayin tattaunawarsa a taron manema labarai daya gabatar domin mayar da martani ga wannan gargaɗi da Amurka tayi, Ministan yace  irin wannan matakin ya saɓawa tsarin diflomasiyya tsakanin ƙasashe.

Ya ƙara da cewa ba laifi bane don sun shaidawa mutanensu abinda suka gani, amma ya kamata Amurka tayi takatsantsan don kada su jefa su cikin ruɗani.

Ministan yada labaran yayi  kira ga masu amfani da shafukan sada zumunta dasu zama masu kishin ƙasa da kuma yaɗa labaran gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *