Kotu ta hana gwamnatin Kano daukar duk wani mataki a kan makarantun firamare da sakandare masu zaman kansu a jihar.

Wata babbar kotun jihar Kano ta hana gwamnatin jihar daukar duk wani mataki a kan
makarantun firamare da sakandare masu zaman kansu a jihar.

Mai shari’a Nasiru Saminu ne ya bayar da umarnin na hana gwamnati ci gaba da yunkurin
daukar wani mataki a halin yanzu bayan sauraron karar da Barr AbdulHafees D. Khalid ya
shigar yana neman kotun ta dakatar da gwamnatin.

Wadanda suka nemi a shigar da kara sun hada da kungiyar amintattu na kungiyar Model Islamic
Schools, Nigeria, Incorporated Trustees of Independent School Proprietors’ Association
Kano, Incorporated Trustees of the National Proprie of Private Schools Kano Chapter,
Incorporated Trustees of Association of Private Schools.

Da kuma sauran mamallakan makarantu masu zaman kansu a fadin Jahar,inda suke bukatar
gwamnatin ta dakatar da yunkurin hanasu lasisin gudanarwa kamar yada tayi niyyar yi.

Yayin da wadanda ake kara sun hada da gwamnatin jihar Kano, gwamnan jihar Kano, da
babban lauyan gwamnatin jihar Kano, da hukumar kula da masu zaman kansu da ayyukan
sa kai ta jihar Kano, da kuma Comrade Baba Abubakar Umar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *