Faransa za ta dawowa Nigeria dala miliyan 150 na kuɗin da Abacha ya boye

Fadar shugaban Kasa ta ce Faransa za ta dawo wa Nigeria dala miliyan 150 na ku ya karɓi
bakuncin ministar Turai da harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna, a fadarsa da ke
Abuja.

Tinubu ya ce ya ji daɗin labarin dawowa Najeriya kuɗin Abacha da Faransa ke shirin yi, inda ya ce
za a yi amfani da kuɗin wajen samar da ci gaba a ƙasar.

Shugaban ya kuma yi farin ciki da irin ƙaruwar hulɗar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu,
musamman ma a ɓangaren sauyin yanayi, ci gaban tattalin arziki, ilimi da kuma raya al’adu.

Tinubu ya kuma yaba da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar Yuro miliyan 100 tsakanin Najeriya
da Faransa don tallafawa shirin i-DICE – wani shiri na Gwamnatin Tarayya na inganta zuba jari
a Fasahar Sadarwa da kuma Masana’antu na Fasaha.

Ministan sadarwa da kirkire-kirkire, Dr Bosun Tijani, da ministan harkokin kasashen waje na
kasar Faransa ne suka rattaƁa hannu kan yarjejeniyar a wani taro da aka yi a gidan Tafawa
Ɓalewa, a hedkwatar ma’aikatar harkokin wajen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *