Dakarun Rundunar sojin Najeriya sun kashe ‘ƴan bindiga 4 a ƙauyen Kampanin Doka dake Kaduna

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ƴan bindiga huɗu a ƙauyen Kampanin Doka a
karamar hukumar birnin Gwari na jihar Kaduna.

Wata sanarwa da sojojin suka fitar, ta ce sun samu nasarar kashe ƴan bindigar ne a ranar 1 ga watan
Nuwamba a wani samame da suka kai ƙauyen.

Sojojin sun ce sun kwato bindigar AK 47, da harsasai, da adda guda ɗaya, wayar tarho, da kuma babura 14 daga hannun ɓata-garin.

A wani samame na daban da sojojin suka yi ranar 2 ga watan Nuwamba a ƙauyen Sabon Sara, sun ce sun
kashe wani ɗan bindiga ɗaya, wasu kuma suka tsere da raunukan bindiga, bayan da wasu manoma suka
kai musu rahoton ganin ƴan bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *