Sheikh Gumi: “Akalla ‘yan Najeriya 2,497 sun bayar da sama da Naira miliyan 17 ga Falasdinawa da suka jikkata a yakin Isra’ila da Hamas a Gaza”

Sheikh Ahmed Abubakar Mahmud Gummi ya ce za a bayar da kudaden ne ta hannun kungiyar agaji ta Red Cresent ga wadanda yakin Gaza ya shafa.

An bayar da tallafin ne bayan wani kira da babban malamin addinin nan na Kaduna, Ahmad Gumi ya yi a ranar Alhamis, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su taimaka wa Falasdinawa.

Malam Gumi ya bayar da gudunmawar Naira 50,000 da kansa a lokacin da yake kaddamar da neman kudi.

Limamin masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, Muhammed Suleiman, ya ce bayan rokon da aka yi, an tara jimillar kudi Naira miliyan 17,959,806 domin tallafa wa al’ummar Falasdinu.

Bayan kudin roko, ta hannun gidauniyar masallacin Sheikh Abubakar Gumi, da kuma Dr. Ahmad Gumi Student’s Forum Account an tara kudaden da aka ambata cikin kwanaki bakwai.

Aƙalla ‘yan Najeriya 2,497 ne suka ba da gudummawar a asusun roko tare da mafi ƙarancin masu ba da gudummawar da ke aikawa a cikin N50 da kuma mafi girman gudummawar N100,000.

Manufar ita ce a taimaka wa wadanda yakin ya rutsa da su wanda ya hada da yara da raunana a Gaza, wannan shi ne abin da za mu iya ba su bayan addu’a,” in ji Malam Suleiman.

Malam Suleiman ya ce za a bayar da kudaden ne ta hannun kungiyar agaji ta Red Cresent ga wadanda yakin Gaza ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *