Jami’ar Nassarawa ta amince da daukar ‘yan banga guda 20 domin yaki da ta’addanci

Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) ta dauki wani muhimmin mataki na yaki da ta’addanci ta hanyar amincewa da daukar ‘yan banga guda 20 da za a tura cikin dabara a wurare daban-daban da ba a cikin harabar jami’ar ba.

Farfesa Abdullahi Modibbo mataimakin shugaban jami’ar ta NSUK, ya bayyana a wata hira da manema labarai a kwanakin baya cewa jami’ar ta kuduri aniyar dakile matsalar garkuwa da mutane da kuma tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikata da dalibai.

“Sace mutane abin damuwa ne ga mahukuntan jami’ar duk da cewa mun san matsala ce ta kasa baki daya.

“Ga wadanda ke harabar jami’ar, ba mu da matsala sosai saboda muna aiki tare da hadin gwiwar jami’an tsaron Najeriya na Civil Defence.

“Ga wadanda ke wajen harabar jami’ar, mun amince da daukar ’yan banga guda 20 wadanda za a horar da su dabarun gudanar da ayyukansu a lungu da sako na wurare daban-daban a wajen harabar.

“Wannan na daya daga cikin kokarin da muke yi na tabbatar da tsaron ma’aikata da daliban,” in ji Modibo.

JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa a baya-bayan nan ne masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da wasu dalibai da malaman makarantar tare da sakar su bayan an biya su kudin fansa.

A kwanakin baya, Dakta Monica Adokwe, wata malama a tsangayar gudanarwa ta jami’ar, ta samu ‘yanci bayan an biya wadanda suka sace ta wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *