Gwamnatin tarayya ta bukaci Isra’ila ta bari a shiga da kayan agaji ga miliyoyin Falasɗinawa

Gwamnatin tarayya ta bukaci Isra’ila ta bari a shiga da kayan agaji ga miliyoyin Falasɗinawa da hare-harenta a ya raba da muhallansu.

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya ce rikicin ya jefa fararen hula da ba su da hannu a kansa cikin mawuyacin hali, yana mai kira ga Isra’ila ta bari a shiga da kayan agajin jinkai Zirin Gaza.

Ministan ta wata sanarwa a ranar Asabar ya jaddada kira da a aiwatar da tsarin kasashe biyu na Falasdinawa da na Isra’ila masu cin gashin kansu don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.

Ya bayyana cewa “Najeriya na kara kira da a gaggauta tsagaita wuta a koma kan teburin sulhu don samun mafita ta lumana, sannan a aiwatar da tsarin kasashe biyu masu cin gashin kansu don warware rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa”.

Kiran na zuwa ne mako uku bayan Isra’ila ta ƙaddamar da hari a yankunan Falasɗinawa a Zirin Gaza inda ta kashe mutum akalla 7,000, akasarinsu kananan yara da mata, daga ranar 7 ga Oktoba.

Mako guda kuma ke nan da aka fara shigar da kayan agaji ta kasar Masar, sakamakon hana shiga da fita da Isra’ila ta yi a Gaza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *