Buhari yayi watsi da jita jitar da ake yadawa cewa ya gurfanar da Rarara a gaban kotu

Tsohon  shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi watsi da jita jitar da ake yadawa cewa ya gurfanar da Mawakin nan Dauda Kahutu Rarara a gaban kotu saboda zarginsa da yi masa kazafin cewa Buharin ne ya rusa kasar nan.

Idan za,a iya tunawa a wani taron manema labarai da Dauda Kahutu Rarara yayi ,ya zargi tsohon shugaban kasa Buhari da lalata kasa da kuma gurgunta tattalin arzikin Najeriya,inda Dauna Rarara din yace yayi nadamar goyon bayan Buhari a zaben da akayi masa karo na farko da karo na biyu,koda yake Yan Najeriya da dama sun zargi Rarara din da yiwa Muhammadu Buhari Butulci.

Amma a wani martani da tsohon shugaban kasa Buhari yayi kan wasu labarai da suke fita a shafukan sada zumunta na zamni cewa Buhari ya gurfanar da Dauda Kahutu Rarara a gaban Kotu dan neman hakkinsa kan kazafin da yayi masa,yace bashida wata Niya na kaishi kara ko daukar mataki akan Rarara din.

A wata tattaunawarsa da Rahma Radio a safiyar Lahadin nan tsohon mai taimakawa Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kafafen sada zumunta Malam Bashir Ahamad yace Kamar ko wanne dan Najeriya Dauda Rarara yana da yancin fadin albarkacin bakinsa kan salon mulkin Buhari.

Bashir Ahamad yace zamani ne na Demokaradiya kuma abinda Rarara din yayi idan tana kan hanya yan kasa zasu fi kowa sani idan kuma ta kauce hanya nan ma zasu fahimta.

A karshe Tsohon shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari ya roki yan kasar nan da suyi watsi da maganar cewa ya gurfanar da Rarara a gaban kotu,yana mai cewa a baya wasu sunyi abinda yafi nasa akan shugabannin da suka wuce ciki hardashi kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *