Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 350

Gwamnan ya ce kudirin kasafin kudin da aka gabatar mai taken ‘Budget of Restoration and Transformation’ zai sauya al’amura a Kano

Da yake gabatar da kididdigar kasafin ga ‘yan majalisar a ranar Juma’a, Yusuf ya yi alkawarin toshe yadda ake bankado kudaden jama’a.

Yusuf ya ce daga cikin kasafin kudin da aka kiyasta na Naira biliyan 350.2, an ware Naira biliyan 215.8 ne domin gudanar da manyan ayyuka yayin da aka ware Naira biliyan 134.4 don kashe kudade akai-akai.

Kasafin kudin ya nuna cewa ilimi ya samu kaso mafi tsoka da Naira biliyan 95.3.

Ayyuka sun samu Naira Biliyan 40.4, Aiyuka na musamman Naira Biliyan 5.1, sufuri Naira Biliyan 4.8 yayin da aka ware Naira Biliyan 11 na Noma.

Hakazalika an ware kudaden ruwa Naira biliyan 13.4 yayin da mata da matasa suka samu Naira biliyan 8.9.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin sa na mai da hankali wajen bunkasa jarin dan Adam, inganta rayuwar al’ummar Kano baki daya, tsaro, kiwon lafiya, samar da abinci da ayyukan yi da dai sauransu.

Muna cigaba da daukar matakai wadanda zasu ciyar da al’ummar jahar Kano gaba nan bada jimawa ba kuma zamuyi amfani da wannan kasafin kufi na bana wajen amfanin gaba daya al’ummar jahar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *