“Babu wata al’umma a jihar da har yanzu ke karkashin Boko Haram” – Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Juma’a, ya ce babu wata al’umma a jihar da har yanzu ke karkashin ikon ‘yan ta’addan Boko Haram, inda ya ce an samu saukin matsalar tsaro da sama da kashi 85 cikin dari.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawar sirri da shugaban kasa Bola Tinubu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Idan za a iya tunawa, tsawon shekaru da dama, al’ummomin Monguno, da Banki, da Jere, da kuma Domboa a Jihar sun sha fama da ta’addancin ‘yan Boko Haram.

Da yake amsa tambaya kan matsalar tsaro a jihar Borno bisa la’akari da rahotannin rashin tsaro na baya-bayan nan, Zulum ya ce gaskiya matsalar tsaro a jihar Borno ta samu sauki da fiye da kashi 85 cikin dari.

Ana ci gaba da gudanar da harkokin tattalin arziki yadda ya kamata a jihar Borno.

Na karanta wasu rubuce-rubuce a kwanakin baya na cewa tashin hankali na karuwa a jihar Borno. Labarin bai dace ba. Sojojin Najeriya na ba mu hadin kai da ake so, ‘yan sanda, jami’an tsaro da na sama da sauran sassan sojojin Nijeriya suna tallafa mana.

Amma abu mafi mahimmanci, ina so in tabbatar muku cewa a matsayina na babban jami’in tsaro na jihar Borno, jihar na samun ci gaba ta fuskar tsaro.

Akwai babban ci gaba a yanayin tsaron mu. Kuma ina yaba wa hafsoshin tsaro bisa kokarin da suke yi, ina kuma yaba wa shugaban tarayyar Najeriya.

Da aka tambaye shi ko yana mai tabbatar da cewa komai ya daidaita ga daukacin kananan hukumomin da a baya suke karkashin ikon ‘yan tada kayar baya, gwamnan ya ce a maganar gaskiya babu ko daya daga cikin kananan hukumomi 27 na jihar Borno da ke karkashin ikon ‘yan tada kayar baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *