Ƙungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano ta sanar da ƙarin farashin kwai

Ƙungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano ta sanar da ƙarin farashin kwai sakamakon tashin gwauron zabin da abincin kajin ya yi.

Ƙungiyar ta ce bayan nazari da lissafin da mambobinta suka yi kan yadda suke tafiyar da sana’ar tasu, sun cimma matsayar sanar da sabon farashi inda ta ƙara da cewa abincin kaji mai iganci a yanzu ya haura naira 11,000 a kan ko wanne buhu.

Shugaban ƙungiyar, dakta Usman ya ce idan ba su ƙara farashin ƙwan ba, babu riba.

Ya kuma jadadda cewa sabon farashin shawara ce da suka bai wa junansu, ba umarni ba.

Masu kiwon kajin sun ce babban abin da ake hada abincin kajin da shi, wato masara ta yi tsada, lamarin da ya sa wasu ma ke dakatar da aiki.

Za ku iya sauraron rahoton Zahraddeen Lawan daga kano kan wannan batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *