Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama wani da ake zargi da  sayar da filayen Gwamnati guda 632

Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano PCACC ta ce ta kama wani Musa Salihu Ahmed da laifin sayar da filayen Gwamnati guda 632 akan yaudara da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 2.3 a fadin Jihar.

Shugaban hukumar Muhuyi Magaji ya bayyana haka ga manema labarai a Kano ranar Talata.

Mista Magaji ya ce an kama wanda ake zargin ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano jim kadan da saukarsa daga kasar Saudiyya.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin yana amfani da Lamash a matsayin kamfani yana sayar da filayen akan kusan Naira miliyan 25 kowannensu ga daidaikun mutane a Challawa da ke karamar hukumar Kumbotso a Jihar.

Hakazalika ya ce wanda ake zargin ya sayar da filaye daban-daban na mazauna garin Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa.

A yanzu haka muna kan bincike akan wanda ake zargin tare da mamakin yadda a zamanin Gwamnatin da ta shuɗe aka ware masa filaye guda 632 kuma an sayar da shi ga mutane daban-daban a Jihar.” Inji shugaban.

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *