Gwamnatin Tinubu  na shirin sake  ciyo sabon bashin na naira tiriliyan 26

Gwamnatin shugaban kasa Bola Tunubu  na shirin sake  ciyo sabon bashin na naira tiriliyan 26, inda jumullar bashin da za a bi Najeriya muddin aka bada wannan sabon bashi zai tasamman naira tiriliyan 100 da  18 .

Bincike ya tabbatar dacewa an samu wannan  adadi ne sakamakon nazari da aka yi a kan bashin da ake  bin kasar a halin yanzu da kuma wanda take hasashen ciyowa daga shekarar 2024 zuwa 2026.

Kamar yadda sabon manufar Bola Tunubu ta  nuna akan  kudi gwamnatinsa  na shirin karbar rancen naira tiriliyan 26 da biliyan 42 a tsakanin shekarar 2024 da 2026, kana  shugaban zaiyi amfani da naira tiriliyan 29.92 a cikin shekaru  3 wajen biyan kudin ruwa na basukan da ake bin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *