“Gwamnatin Najeriya na alfahari da Dangote kan yadda yake inganta tattalin arzikin kasar” – Tinubu

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya na alfahari da Dangote kan yadda yake inganta tattalin arzikin kasar nan.

A jiya ne kamfanin Dangote ya samu gagarumar lambar yabo daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya bayyana matsayin gwamnati kan ci gaban da kamfanin ya samu a Nijeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.

Dangote dai shi ne babban mai daukar ma’aikata bayan gwamnati, kuma daya daga cikin manyan masu hannu da shuni a nahiyar.

A jawabin da ya gabatar tun farko lokacin da yake bude taron shekara-shekarar, shugaban ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su shiga sahun masu dawo da ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, inda ya kara da cewa kasar za ta iya bunkasa ne ta hanyar hadin gwiwa.

Masana da suka yi jawabi a wajen taron sun bayyana cewa Nijeriya na jiran matatar man fetur ta Dangote, inda suka bayyana kwarin gwiwar cewa hakan zai kawo wani gagarumin ci gaba ga tattalin arzikin kasar nan.

Da yake jawabi a wajen taron mai taken: ‘Bude Hanyar Yaki Da Cin Hanci da Rashawa’, Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin Dangote Industries Limited, Mista Olakunle Alake, ya ce ya yi farin ciki da yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ta fahimci rawar da kamfanoni ke takawa, tare da karfafa bukatar hadin gwiwa.

Mista Alake ya ce dole ne Nijeriya ta bunkasa tattalin arzikinta musamman bangaren masana’antu domin samun damar taka muhimmiyar rawa a yankin Afirka da bangaren ciniki (AFCFTA).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *