Masu zanga-zanga sun taru a Legas don nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasɗinu.

Gomman masu zanga-zanga ne suka taru a birnin Legas don nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasɗinu.

Mutanen maza da mata sun fito ne a jiya Asabar ɗauke da kwalaye iri-iri da ke neman “adalci ga Falasɗinu” da kuma “a bai wa Falasɗinu ‘yanci”.

Da yawan waɗanda suka yi magana a wurin taron sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta ƙaurace wa hulɗa da Isra’ila,da kuma kayan da take sarrafawa .

Kafin Yan Lagos suyi zanga zangar nuna goyon bayansu ga Falasdiniya ,alumar musulmin birnin Paris na kasar Faransa suma sunyi tasu zanga zangar a ranar juma,a data gabata duk dacewa kasar Faransa taso hana zanga zangar amma daga baya kotu a kasar ta basu dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *