Atikun yace babu abinda zai hada Kotun Kolin karbar wasu Sabbin Hujjojin da yake son gabatarwa.

A yayinda a gobe Litinin ake sa ran Kotun Kolin kasar nan zata fara zama kan bukatar Atiku Abubakar na sauke Shugaban kasa Bola Ahamad Tunubu daga kan Kujerarsa,Atikun yace babu abinda zai hada Kotun Kolin karbar wasu Sabbin Hujjojin da yake son gabatarwa.

Atikun yayi wannan magana ce dan mayar da martani kan yadda yace lauyoyin Ahamad Bola Tunubu da jam,iyar APC  suke  maganganu akan Hujjar da Atikun ya rika ta nemo takardun Bogi na karatun shugaban kasa Bola Tunubu daga jami,ar Chikago a kasar Amurika inda suke sukar Atikun cewa ya saki Reshe ya rike ganye.

Saidai Atikun ya kara nanata cewa idan har Kotun Kolin kasar nan ta karbi Hujojinsa da zai gabatar a gabanta daga Gobe Litinin da zaa fara zama,to tuhumar da yake yiwa Bola Tunubu bata rashin cancantarsa ya tsaya takarar shugaban kasa bace kadai,harda Yaudarar yan kasa wajen gabatar da takardar shaidar karatu ta jabu.

Tun a baya wata Kotu a kasar Amurika ta bada umarni ga jami,ar Chkago ta baiwa Atiku Abubakar takardun shaidar karatun Bola Tunubu kamar yadda ya bukata daga Kotun,inda ita kuma jamiar ta fitar da takardun masu shafi 32.

Saidai tun bayan fitar da takardun shaidar kammala jamair ta Chkago da Bola Ahamad Tunubu yace ya kammala shugaban kasa Bola Tunubu da ,Jam,iayarsa ta APC da ita kanta hukumar Zabe ta kasa INEC sukace babu wata kofa ta sake gabatar da sabbin hujjoji a kotun Kolin ta Najeriya.

Sunce adadin kwanaki 180 da aka baiwa mai kara ya gabatar da hujojinsa tun a kotun farko sun kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *