Tinubu ya amince da naɗin Shaakaa Chiraa matsayin sabon Babban mai Binciken Kuɗi na Ƙasa

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Mr. Shaakaa Chira, a matsayin sabon Babban mai Binciken Kuɗi na Ƙasa.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.

Tinubu ya amince da naɗin ne bayan tantancewa da Hukumar Kula da Ma’aikatan Tarayya tayi, inda ta kuma fito da sunan Mr Chira bayan samun maki da ya fi na wadanda aka tantance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *