Motoci dauke da kayan abinci sun samu shiga cikin Gaza

Motocin da ke dauke da kayan agajin jin kai na Gaza da yaki ya daidaita,sun fara tsallakawa kan iyakar Rafah daga Masar a ranar Asabar, kamar yadda wata majiyar tsaro da jami’in kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar ta shaida wa AFP.

Gidan talabijin din kasar Masar ya nuna wasu manyan motoci da ke shiga kofar a rana ta 15 na yakin da ake yi tsakanin Isra’ila da Hamas, kungiyar masu jihadi da ke mulkin yankin Falasdinu mai mutane miliyan 2.4.

Isra’ila ta kai hare-hare a Gaza tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba.

Kungiyar masu kishin Islama ta kutsa kai cikin Isra’ila daga zirin Gaza tare da hallaka akalla mutane 1,400, galibi fararen hula da aka bindige su a ranar farko ta harin, a cewar jami’an Isra’ila, tare da yin garkuwa da mutane fiye da 200.

Isra’ila ta ayyana kakabawa yankin Zirin Gaza gaba daya tare da katse hanyoyin samar da ruwa da wutar lantarki da man fetur da abinci, lamarin da ya haifar da karancin abinci.

Rafah dai ita ce hanya daya tilo ta shiga Gaza da Isra’ila ba ta iko da ita, wadda ta amince da shigar da kayan agaji daga Masar sakamakon bukatar da babbar kawarta ta Amurka tayi.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, manyan motoci 20 ne daga kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar da ke da alhakin kai kayan agaji daga hukumomin MDD daban-daban.

Wani dan jarida na AFP da ke bangaren Falasdinawan da ke mashigar ya ga tireloli 36 babu kowa suna shiga tashar kuma suka nufi bangaren Masar, inda za a yi musu lodin kayan agajin da ke shigowadasu daga kasashen Duniya.

An kuma ga motocin daukar marasa lafiya hudu, motocin Majalisar Dinkin Duniya biyu da na Red Cross guda biyu suna nufar tashar.

Jiragen dakon kaya da manyan motoci sun kwashe kwanaki suna kai kayan agaji zuwa yankin Rafah na Masar, amma kawo yanzu babu wani da aka kai Gaza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *