Hukumar Zaɓen Najeriya, Mai zaman Kanta INEC, ta bayyana cewa kotu ta yi watsi da kararrakin zaɓe 900 daga cikin 1200 da aka shigar kan zaɓukan wannan shekara.
INEC ta ce hakan ya nuna cewa ta samu nasara gudanar da sahihan zaɓukan da suka gabata da aƙalla kashi 74 cikin 100.
Mai magana da ywaun hukumar ta INEC zainab Aminu ta ce wannan wani babban kwarin guiwa ne ga aiyukan hukumar.
Zainab Aminu ta ce idan akai la’akari da Kararrakin zabe da aka shigar gaban kotu na
kararrakin zabe guda dubu daya da dari daya da casa’in da shida, dari bakwai da goma sha biyu, kotun kararrakin zabe ta yi watsi da su sabda ba su da Muhimmanci, hakanan ta ce guda dari da casa’in da tara su kansu wadanda su ka shigar
da karar sun janye su daga baya.
Hukumar zabe Inec ta nesanta kanta daga cikin wadanda ake yawan kaiwa kara kotu bisa hujjar cewa ba su shafe ta ba.
Mai magana da yawun hukumar zabe Inec Zainab Aminu ta ce akwai kuskure cewa kashi casa’in da hudu na kararrakin zaben da aka shigar ana kalubalantar yadda ta gudanar da zabenne alhalin ba hukumar zabe ke da alhakin tantance ‘yan takara ba tunda ba ya cikin aiyukan da su ka rataya a wuyanta.