Gwamnatin tarayya na shirin rukunin gidaje kusan 34,500 a faɗin ƙasa – Minista

Ministan gidaje da raya birane, Architect Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na rukunin gidaje kusan 34,500 a faɗin ƙasa, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin bunƙasa al’ummomi masu ayyukan haɗin gwiwa
a Najeriya.

Arc. Dangiwa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin Gwamnan Jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.

Ya ce biranen da za a gina za su kasance cikin matakai, inda a mataki na farko, ake da niyyar ginda rukunin gidaje 34,500 a cikin jihohi talatin 30 na ƙasar.

Ya ce gidajen za su kuma kasance cikin rahusa domin mutane su samu damar mallaka.

Ministan ya ce don yin haka, ma’aikatar za ta yi da aiki da bankin bayar da rancen gina gidaje na Najeriya (FMBN) don bai wa masu cin gajiyar damar samun rancen gidajen a cikin rahusa, wanda za su iya biya cikin shekaru 3,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *