Akpabio yayi watsi da zargin da Sanata Elisha Abbo yayi na cewar yana da hannu a ƙwace nasararsa da kotu tayi

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio yayi watsi da zargin da Sanata Elisha Abbo yayi na cewar yana da hannu a ƙwace nasararsa da kotun ɗaukaka ƙara tayi a ranar Litinin.

Da yake magana da manema labarai, mai magana da yawun shugaban majalisar ta dattawa, Eseme Eyiboh, yace ba shida hannu a hukuncin da kotun ta yanke.

Eyiboh yace abin takaici ne idan Abbo yayi zargin cewa yana da a ƙwace nasararsa.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar a ƙasarnan na yanke hukunci ne bisa tanadin dokar zaɓe da kuma irin hujjojin da masu ƙara suka gabatar.

Tunda farko, bayan ƙwace nasararsa da kotun ɗaukaka ƙara a Abuja tayi, Sanata Abbo yayi zargin cewa Godswill Akpabio nada hannu a lamarin.

Hukuncin na nufin Abbo yabar Majalisar Dattawan Najeriya kenan kasancewar itace kotun ƙarshe dake da hurumin sauraron ƙorafin zaɓen ‘yan majalisar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *