Sojoji sunyi nasarar kwato dalibai 4 da aka sace A jami’ar Gusau

Dakarun Operation Hadarin Daji na sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an ‘yan sandan jihar Zamfara sun ceto daliban jami’ar tarayya Gusau (FUGUS) guda hudu da aka yi garkuwa da su.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, ya fitar a Gusau ranar Lahadi.

Rundunar sojojin na Operation Hadarin Daji tare da rundunar ‘yan sandan jihar sun ceto daliban jami’ar tarayya Gusau (FUGUS) guda hudu da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su a dakunan kwanan dalibai da ke unguwar Sabongida ranar Asabar.

An samu nasarar ceton daliban ne bayan da sojojin suka amsa kiran da aka yi musu a kan lamarin.

Ba tare da bata lokaci ba sojojin suka tattara tare da kafa wani shinge akan hanyar wanda yasa akayi dauki ba dadi tsakanin sojojin Nijeriya da barayin dajin.

Daga nan ne muka fi karfinsu sai ‘yan ta’addan sun yi watsi da wadanda lamarin ya rutsa da su da misalin karfe 12 na dare, inda daga bisani sojoji suka kubutar da su Yahaya ya bayyana.

A baya-bayan nan ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da dalibai 25 ‘yan makaranta guda da ma’aikatan gine-gine 9 da ke unguwarsu daya.

Jami’an tsaro sun ceto dalibai 13 da ma’aikatan gine-gine 3 yayin da sauran wadanda harin ya rutsa da su na hannun ‘yan bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *