Gwamnatin tarayya zata ciwo bashin kudi dala miliyan 400 daga Bankin Duniya domin rabawa yan Najeriya

Gwamnatin tarayya zata ciwo bashin kudi dala miliyan 400 daga Bankin Duniya domin rabawa yan Najeriya kudaden .

Gwamnatin tace za,a ciwo wannan bashi kudin ne , domin tallafa wa magidanta  15 a fadin kasar, nan kamar yadda shugaban kasa Bola Tunubu ya yi alkawari matakin da ta ce zai ragewa  marasa karfi radadin cire tallafin man fetur .

Karin rancen na Dala miliyan 400 da Najeriyar ta nema dai zai sanya jimillar bashin da  ta karba daga bakin duniyar kai wa Dala miliyan dubu 1  da Dala miliyan 200, la’akari da cewar a baya bayan nan bankin ya amince da baiwa Najeriya  Dalar miliyan 800, wanda su ma ta ce za ta raba wa marasa karfi, don saukaka musu matsin tattalin arzikin da suka shiga bayan Cire tallafin man fetur.

A ranar 1 ga watan Oktaba, yayin jawabi kan murnar zagayowar ranar da Najeriya ta samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka, shugaba Bola Tinubu ya sanar da shirin raba wa magidanta miliyan 15 kudi ta hanyar aike musu da tallafin ta asusunsu na banki, domin saukaka musu hauhawar farashin kayayyakin da suke fuskanta, saboda cire tallafin man fetur.

A karshen wannan watan ne Magidanta din Miliyan 15 zasu fara samun naira dubu 25 duk wata na tsawon watanni Shida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *