Tinubu ya bayyana shirin da gwamnatinsa take na ganin cewar Malaman makaranta sun samu kulawar data dace.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin da gwamnatinsa take na ganin cewar Malaman makaranta sun samu kulawar data dace.

Shugaban kasa  Ya nuna rashin jin dadinsa a kan matsalolin da suke addabar Malaman makaranta a Nijeriya da suka hada da cunkoso a cikin azuzuwa da  rashin yadda za a inganta  aikin malaman makaranta a fadin nigeria wanda acewarsa hakan ya faru ne saboda rikon sakainar kashin da aka yi wa aikin Malanta.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu  ya bayyana hakan ne a bikin ranar  Malaman makaranta ta duniya na shekarar 2023 wanda Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilce shi a Eagle Skuare.

Idan dai ba a manta ba a shekarar 2020 ne Shugaban kasa a wancan lokacin Muhammadu Buhari ya amince da tsarin albashi na musamman ga Malaman makarantun Firamare da Sakandare, wanda ya  hada da bada alawus- alawus na Malaman kimiyya wadanda aka tura kauye, bugu da kari kuma ya kara shekarun aiki na Malaman makaranta daga 35 zuwa 40 da  lokacin ritaya zuwa shekara  65.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *