“Shugabanci mara kyau da son kai na daya daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta” – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana shugabanci mara kyau da son kai a matsayin daya daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Wike ya bayyana haka ne yayin da yake lura da cewa an kafa dokar da ta kafa hukumar ma’aikata ta FCT amma har yanzu ba a aiwatar da ita ba.

Ministan ya ce ya tunatar da shugaban kasa Tinubu dangane da dokar da ta ayyana hukumar ma’aikatan gwamnati na babban birnin tarayya Abuja,kuma ya amince da  a kaddamar da dokar inji shi.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma’a, Wike ya ce daya daga cikin matsalolin kasar nan shi ne shugabanci, don haka mutane da yawa ba sa son daukar mataki saboda gudun surutun al’umma..

A shekarar 2018, Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da kudirin doka wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya amince da ita  lokacin da yake rike da mukamin mukaddashin  shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *