Majalisar Dattijai na neman a ci tarar naira 50,000 ga iyayen da suka gaza bai wa ‘ya’yansu ilmin firamare da sakandire.

Majalisar Dattijai ta yi karatun farko ga wani ƙuduri da ke neman a ci tarar naira 50,000 ga iyayen da suka gaza bai wa ‘ya’yansu ilmin firamare da sakandire.

 Majalisar ta kuma buƙaci a riƙa bai wa kowanne yaro abinci kyauta a Najeriya.

Ƙudurin wanda Sanata Orji Kalu ya gabatar mai taken ‘Dokar ba da ilmi kyauta kuma dole a matakin farko ga kowa ta 2004, Sashe na 2, na cewa kowacce gwamnati a Najeriya ta samar da ilmin bai ɗaya kyauta kuma dole ga duk yaron da ke cikin shekarun shiga firamare da ƙaramar sakandire.

Dokar ta kuma bayyana cewa masu ruwa da tsaki a fannin ilmi cikin ƙananan hukumomi su tabbatar cewa dukkan iyaye ko wani mutum da ke kula ko riƙon wani yaro, ya sauke nauyin da aka ɗora masa a ƙarƙashin sashe na 2, ƙaramin sashe na 2 na wannan Doka.”

Ƙudurin ya kuma yi nuni da cewa matuƙar mahaifi ya saɓa wa tanadin da aka zayyana tun farko, to ya aikata laifi, kuma idan aka same shi da laifi a karon farko, a tsawatar masa.

Sai dai yanzu Majalisar Dattijai a gyaran fuskar da take ƙoƙarin yi, tana yunƙurin sauya tarar naira 5,000 da ke cikin dokar zuwa naira 50,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *