Gwamnatin tarraya: N-Power za ta biya bashin watanni 8 nan ba da jimawa ba

Ma’aikatar jinkai da yaki da Talauci ta tarayya ta baiwa wadanda suka ci gajiyar shirin N-power tabbacin biyan basussukan watanni 8 da aka rike musu.

Manajan shirye-shirye na N-Power Akindele Eghuwalo ne ya bayyana haka bayan taron da suka yi da wakilan wadanda suka ci gajiyar shirin na N-Power.

“Abin farin ciki shi ne cewa a jiya an kwato kudaden kuma za ku samu kudaden ku nan ba da dadewa ba.

“Za a fara biyan bashin masu cin gajiyar N-Power Batch C na watanni takwas nan ba da jimawa ba,” in ji shi.

Akindele ya ci gaba da bayyana cewa, ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr Betta Edu, ta dukufa ba dare ba rana domin kamo wasu kura-kurai a cikin shirin da sauran shirye-shiryen zuba jari na zamantakewa.

“Wadannan rashin bin ka’ida sun sa talaka ya daina amincewa da iyawar Gwamnati na samar da kariya ga al’ummarta amma Dr Betta Edu tana daukar duk matakan da suka dace don magance wadannan matsalolin tare da isar da Sabbin Fatan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ga ‘yan Najeriya,” ya tabbatar.

“Yawancin kura-kurai da suka kawo cikas wajen aiwatar da shirin ana magance su. Idan dai ba a manta ba a lokacin da aka fara aikin an lura cewa da yawa daga cikin wadanda suka ci gajiyar aikin ba sa karbar kudaden alawus-alawus din su na wata-wata, yayin da masu ba da shawara na kula da tsarin rajista da biyan kudi ke rike da kuɗaɗen wanda kwangilarsa ta ƙare.

“Labari mai dadi shine an kwato kudaden kuma hakan zai ba da damar biyan wadanda suka ci gajiyar kudin.”

Wannan da ma wasu kura-kurai ne da mai girma Ministan ta kuduri aniyar warwarewa ta yadda za a samar da kyakkyawan tushe wanda Renewed Hope N-POWER zai fadada har ya kai matasa miliyan 5 a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *