Gwamnan Kano ya rattaba hannu kan karin kasafin kudin 2023 na naira biliyan 58.

Gwamnan Kano ya ce karin kasafin kudin na da nufin kula da ayyukan samar da ababen more rayuwa da kasafin 2023 bai kunshe su ba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sa, Bature Tofa, ya fitar a nan Kano, a ranar Asabar.

Gwamna aAbba kabir  Yusuf ya tabbatar da cewa  gwamnatinsa za ta bi ka’idojin kasafin kudi domin za a yi amfani da kudaden da aka ware ta hanyar da ta dace.

Tun da farko kakakin majalisar dokokin jihar Jibrin Falgore wanda ya jagoranci manyan jami’an majalisar da kwamitin rabon kudaden ya gabatar da kudirin amincewar gwamnan a gidan gwamnatin Kano da ke Africa House.

Majalisar dokokin jihar Kano a ranar Litinin ta zartas da karin kasafin kudi na naira biliyan 58, bisa bukatar da gwamnan ya aike musu a ranar 25 ga watan Satumba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *