Najeriya ta kwaso ’yan kasarta sama da 300 da suka makale sakamakon fada tsakanin Isra’ila da mayakan Falasdinawa.

Najeriya ta kwaso ’yan kasarta sama da 300 da suka makale a yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin Isra’ila da mayakan Falasdinawa.

Najeriya ta kwashe su ne bayan da suka tsallaka zuwa kasar Jordan, daga Isra’ila inda suka kai ziyarar ibada daga Jihar Legas.

An kwashe ’yan Najeriyar masu ziyarar ibada a Isra’ila ne a yayin da dubban ’yan kasashen waje suka makale a Isra’ila da Falasdinu sakamakon yakin bangarorin da ya shiga kwana da biyar.

Akalla mutum dubu uku ne suka rasu, wasu kimanin dubu hudu suka jikkata daga gangarorin biyu; lamarin da ya sa kasashe rububin kwashe ’yan kasashen da ke can zuwa gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *