“Mun samu ƙarin jirage samfurin Diamond-62 (DA-62) guda 2”

Rundunar sojin sama ta Najeriya tace ta samu ƙarin jirage samfurin Diamond-62 (DA-62) guda biyu.

Babban hafsan sojin sama na Najeriya, Air Marshal Hassan Abubakar ne ya bayyana hakan a wani takaitaccen biki da aka gudanar a Ilorin na jihar Kwara.

Da ya ke kaddamar da Jiragen, babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya ya bayyana cewa jiragen biyu na cikin jiragen yaƙi hudu da gwamnatin tarayya ta siyo shekara biyu da suka wuce kuma jiragen na farko sun iso tsakanin watannin Fabrairu da Yulin 2023 kuma tuni aka fara amfani da su wurin inganta tsaro a ƙasar.

A yayin da yake kira ga jami’an da za su kula da jiragen da su yi aiki cikin kwarewa, Air Marshal Abubakar ya gargade su da su kuma tabbatar da gudanar da aiki da jiragen yadda ya kamata domin inganta ayyukan rundunar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *