Romania da Hungary sun kwashe ‘ƴan kasar su daga Isra’ila

Ma’aikatar harkokin wajen Romania ta sanar a safiyar yau Litinin cewa, kasashen Romania da Hungary sun kwashe ‘yan kasarsu 460 daga Isra’ila, sakamakon hare-haren wuce gona da iri da ‘yan ta’addan Gaza ke kaiwa.

An kwashe mutane 245 daga Isra’ila zuwa Romania.

Jirage hudu sun tashi daga Isra’ila, biyu daga kamfanin jirgin saman TAROM mallakar gwamnati, wasu biyu kuma na kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu.

Rukunoni biyu na alhazai na daga cikin wadanda aka kwashe.

A halin da ake ciki kuma, an kwaso ‘yan kasar Hungary 215 daga Tel Aviv a cikin jiragen soji guda biyu bayan wani kazamin harin da mayakan Hamas suka kai kan Isra’ila.

A safiyar yau litinin ne jiragen sojojin saman kasar Hungary suka sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Budapest kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Péter Szijjártó ya bayyana a shafin Facebook.

Jiragen biyu na Airbus A319 da aka yi amfani da su sun kasance a matsayin jirage na jiran aiki ga gwamnatin Hungary

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *