Babban Hafsan Sojoji: Bazan baiwa ‘yan Najeriya kunya ba.

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sha alwashin ba zai bari ‘yan Najeriya da shugaban kasa Bola Tinubu su yi kasa a gwiwa ba, a yunkurinsa na samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar nan ta hanyar yakar matsalar rashin tsaro.

Musa ya kuma kara tabbatar da kiyaye akidu da ka’idojin da ke jagorantar rundunar sojojin Najeriya, yayin da ya bukaci sojoji da cewa ya zama wajibi a tabbatar da cewa kowane soja ya sadaukar da kansa.

Ya yi magana ne a wajen taron biki na cika shekaru 38 na godiyar kammala aiki na hafsan sojin kasa na baya-bayan nan, Laftanar-Janar. Faruk Yahaya (Rtd) a matsayin Babban Jagoran kwasa-kwasan da aka yi a Abuja ranar Lahadi.

Dimokuradiyya ta ruwaito cewa taron wanda ya fara a daren ranar Asabar ya samu halartar manyan jami’an soji daga rundunonin soji uku da suka hada da Sojoji da na ruwa da na sama.

Musa ya bayyana cewa nasarar da aka samu a jarkar tsaron Najeriya bai rasa nasaba da goyon baya da kuma amincewa da tsaffin sojojin da suka yi, ya kasance ginshikin tsaron kasar.

Ina fadin hakan daga cikin zuciyata kuma nayi muku alkawarin cewa ba zan baku kunya ba za mu yi duk abin da ya kamata don ganin mun ci gaba daga inda kuka tsaya, domin mu samu cimma burin da ake so na samar da dawwamammen zaman lafiya a kasarmu ta Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *