Tsohon ministan sufurin jiragen sama ya bukaci Tinubu da ya sauka daga kan mukaminsa a mutunce

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya sauka daga kan mukaminsa a mutunce saboda zargin badakalar takardun karatunsa.

Osita na mayar da martani ne a kan maganar da maga takardar  Jami’ar Jihar Chicago  da ke Amurka, Caleb Westberg, ya yi cewa takardun da Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a zaben 2023 ba na makarantarsu ba ne,koda yake daga baya kuma an smau maganganu masu cin karo da juna,inda daga baya kuma jam,air tace takardun na Tunubu sahihai ne.

Westberg ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayar da martani a kan bukatar dan takarar PDP na Shugaban Kasa a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar ya yi, na neman a fitar masa da takardun Tinubun a can.

Atiku dai ya bukaci makarantar ta fitar masa takardun Tinubun ne saboda ya tabbatar da zargi kan badakalar karatun da yake yi masa.

Da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels, Osita ya ce batun abin kunya ne ga kasa baki daya wanda bai kamata a manta da shi haka kawai ba.

Ya kuma yi kira ga Shugaban Kasar da ya kare kasar daga kara fadawa cikin abin kunya, inda ya bukaci Kotun Koli da ta yi abin da ya dace.

Tsohon Ministan ya ce abin damuwa ne kasancewar hukumar tsaro ta DSS da INEC da ofishin jakadancin Najeriya a Amurka da ke Washington ba su iya gano badakalar ba, sai suka bar wa Atiku aikin shi kadai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *