Tinubu, ya yi watsi da bayanan da Atiku Abubakar ya yi yanada isasshiyar shaidar da za ta tabbatar wa kotu cewa ya gabatar da takardar shaidar karatun digiri ta bogi ga hukumar zabe.

Shugaban Kasa  Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da bayanan da abokin takararsa na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, ya yi, cewa ya tattara isasshiyar shaidar da za ta tabbatar wa kotu, cewa shugaban kasar ya gabatar da takardar shaidar karatun digiri ta bogi ga hukumar zabe.

Shugaban Najeriyar, ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe, dangane da gabatar da wata hujja, idan ma akwai ta a shari’ar zaben shugaban kasa.

Cikin wata hira da manema labarai mai magana da yawun shugaban kasa Kan wallafa labarai a jaridu Abdul’Aziz Abdul’Aziz, ya ce abin da shi tsohon mataimakin shugaban kasa ya fada su a wajensu abu ne na su tausaya masa.

Abdul’aziz Abdul’aziz, ya ce ita jami’ar da ake magana a kanta ta jihar Chicago da ke kasar Amurka a dukkannin takardu da bayanai da suka ba wa kotu babu inda suka ce akwai takardar bogi ko kuma shi Tinubu bai yi karatu a wajensu ba.

Mai magana da yawun Shugaba Tinubun, ya ce babu wata magana ta a zo a gani, borin kunya ne irin na wanda ya sha kaye.

Abdul’aziz, ya ce, idan Atiku Abubakar na tunanin ya samo wata hujjar da yake gani zai iya gabatarwa ai bakin alkalami ya riga ya bushe.

Mai Magana da yawun shugaban na Najeriya, ya ce ya kamata yanzu Atiku Abubakar ya gane cewa an rufe babin siyasa kamata ya yi a fuskanci babin gina kasa kawai kamar yadda shi Shugaba Tinubu ya sha fada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *